16 Oktoba 2021 - 17:30
​Isra’ila Ta Fara Jin Tsoron Dorewar Kawancenta Da Kasar Sudan

Wata jiridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta bada labarin cewa gwamnatin kasar ta fara jin tsoron yiyuwar kasar Sudan ta dawo daga rakiyarta, a kawancen da ta kulla da ita a shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kafin haka dai ministan harkokin wajen kasar Sudan Mariam Al-Mahdi ta bayyana rashin amincewar kasar Sudan da matakin da Musa Faki Mohammad, shugaban majalisar gudanarwa na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya dauka na bawa HKI damar zama mamba mai sanya ido a cikin kungiyar, ba tare da tuntubar sauran kasashen kungiyar ba. Ministan ta kara da cewa hakan ya sabawa kudurorin da aka gina kungiyar tarayyar Afirka a kansu.

Jaridar Ma’ariv, ta kammala da cewa a lokacinda kasar Sudan ta rattaba hannun kan yarjejeniyar kawance da HKI a shekarar da ta gabata, an yi maganar za ta kulla wasu karin yarjeniyoyi da ita daga baya, amma har yanzun hakan bai faru ba.

342/